Taɓarɓarewar ilimi a Bauchi: Al’umar Rafin Tambari na neman ɗaukin gaggawa
Daga Sabiu Abdullahi
Yanayin da firamaren Rafin Tambari da ke bayan rukunin gidaje na Tambari a birnin Bauchi, fadar jihar Bauchi, me ciki a halin yanzu, ya saɓa da ikirarin gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad na kashe biliyoyin naira wajen ginawa da kuma kwaskwarima wa ɗakunan karatu sama da dubu biyar a faɗin jihar Bauchi.
Mun ziyarci farfajiyar makarantar domin neman ƙarin haske game da lalacewar da makarantar firamarensu ta yi.
Duk da koke-koke da al’ummar suka yi na tsawon shekaru bakwai, da alama gwamanti ba ta waiwaye su ba har yanzu, duk da cewa ta yi ikirarin gyara bulok na ajujuwa 5,000 a fadin jihar.
TCR ta fahimci cewa rashin rufin kwano a ajujuwan yana tilasta wa ɗalibai rashin rashin halartar darussa a lokutan damina.
Wakilinmu ya tattauna da iyaye, ɗalibai, da sauran al’umma wadanda suka bayyana takaicinsu da rashin jin daɗinsu kan yadda hukumomi suka daɗe ba sa ba su kulawa ta ilimi.
“Sama da shekaru bakwai muna rokon gwamnati ta gyara mana makarantarmu, amma da alama kukanmu bai je ko’ina ba, yaranmu sun cancanci a yi musu abin da ya dace,” in ji wani uba da ya nuna damuwarsa.
“Duk lokacin da aka yi ruwan sama, ajujuwa sai sun zama ba kowa, ana tura yaranmu gida, suna rasa karatunsu, wnada hakan abin takaici ne.”
Matsalar taɓarɓarewar makarantar firamare ta Rafin Tambari, wacce ba ta da ɗalibai kasa da 100, ba wai kawai tana kawo cikas ga karatun yaran ba ne, har ma da game da lafiyarsu.
A cewar wani memba na kungiyar iyaye da malamai (PTA), akwai malamai masu kwazo da suke kokarin zuwa makarantar, amma kokarin da suke yi bai haifar da sakamako mai kyau ba saboda yanayin makarantar.
Kiran neman agajin ya biyo bayan shaidar wadanda abin ya shafa kai tsaye, yayin da suke ba da labarin irin ƙoƙarin da aka yi na jawo hankalin gwamnati kan bukatar gyara cikin gaggawa.
Duk da kasancewarta cibiyar ilimi mai mahimmanci a cikin al’umma, lamarin Makarantar Firamare ta Rafin Tambari ya nuna akwai alamar sakaci, tare da durƙushewar ababen more rayuwa da ke hana neman ilimi ga yara.
Wakilin TCR ya ɗauko mana hotuna masu munin gani na yanayin da azuzuwan biyu kawai na makarantar suke ciki, wanda ke nuna buƙatar kawo agaji cikin gaggawa.
“Abin takaici ne ganin halin da makarantarmu daya ke ciki, muna jin an yi watsi da mu, kuma fatanmu a yanzu ya ta’allaka ga gwamnati ta saurari kokenmu da kuma daukar mataki cikin gaggawa,” in ji wani mai ruwa da tsaki da ya za ta da wakilinmu, wanda kuma ya nemi a sakaye sunansa.
Yunƙurin da Jaridar Citizen Reports ta yi don jin ta bakin jami’in gwamnati don jin ta bakinsa game da lamarin ya ci tura.