January 14, 2025

Sokoto, Katsina wasu jihohi 5 za su yi amfani da sama da naira biliyan 28 don ciyarwar Ramadan

0
images-256.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Yayin da watan Ramadan ke ci gaba da wakana, jihohi bakwai a Najeriya sun ware sama da naira biliyan 28.3 domin ciyar da mazauna yankin a cikin wannan watan mai alfarma.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, jihohin da ke kan gaba a wannan shiri sun hada da Katsina, Sokoto, Kano, Jigawa, Kebbi, Niger, da Yobe.

Yayin da wasu jihohi suka bayyana takamaiman kason da za su kashe, wasu kuma sun zaɓi kada su bayyana ainihin adadin—abin da ya haifar da damuwa game da amana a lamarin.

Malamai da sauran al’umma sun nuna damuwarsu kan dimbin makudan kudade da aka ware domin shirin ciyar da abincin, inda suka bukaci hukumomi da su tabbatar da sa ido sosai domin hana yin amfani da su ta inda bai dace ba.

Yayin da suke ganin muhimmancin tallafa wa masu karamin karfi a watan Ramadanan, sun jaddada bukatar yin taka-tsan-tsan don hana duk wani kokari na lalata tsarin.

Jihar Katsina ce ke kan gaba da kasafin kudin da ya kai naira biliyan 10 domin shirin ciyar da abinci, sai Sokoto da ta samu naira biliyan 6.7, Kano na da naira biliyan 6, Jigawa na da naira biliyan 2.83, Kebbi na da naira biliyan 1.5, Nijar na da naira miliyan 976 da kuma Yobe wacce ke da naira miliyan 178.

Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin da ke sa ido kan rabon kayayyakin, ya bayyana kudirin jihar na tallafa wa ‘yan kasar ta hanyar hakan.

A Sokoto kuma, Gwamna Ahmed Aliyu ya tabbatar da kashe Naira biliyan 6.7 na watan Ramadan da makamantansu, inda ya jaddada jajircewar jihar wajen ciyar da al’ummarta.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Baba Dantiye, kuwa ya yi karin bayani kan kokarin da aka yi, wanda ya hada da kafa cibiyoyi na musamman da kuma samar da kayan abinci iri-iri ga mabuƙata.

Ya ce: “A kowace cibiya, muna da mata uku masu dafa abinci da kuma maza uku da ke samar da tsaro don kada mutane su yi wa abincin dirar mikiya ko kuma su kawo tarzoma.

“A kowace cibiya akwai buhunan shinkafa guda biyu don ciyar da mutane aƙalla 200, wato mutum 100 a kowane buhu; haka kuma akwai nau’o’in abinci irin su ƙosai da kunu da sauran abinci iri-iri da ake dafawa kullum. Kuma ana ba da su tsakanin karfe 6:30 na yamma zuwa karfe 7:00 na yamma wanda aka yi niyya ga mabukata.”

Haka kuma jihar Jigawa na shirin aiwatar da shirin ciyar da abincin ta cibiyoyi 609, inda za a rika yi wa mutane sama da 182,700 a kowace rana, tare da mai da hankali kan manyan makarantu da kuma sayo kayan abinci na gaggawa don tabbatar da wadatar abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *