Sojojin Najeriya sun koka kan rashin biyan su kuɗin alawus a Kaduna
Daga Sabiu Abdullahi
Wasu sojojin da ke karatu a Makarantar Sojojin Najeriya (NASI) da ke Jaji, Jihar Kaduna, sun nuna rashin jin daɗinsu kan rashin biyan kuɗin alawus ɗin su na Ration Cost Allowance (RCA) da kuma alawus ɗin karatu.
A cewar Dokar Gudanar da Kuɗi ta Rundunar Sojojin Najeriya (2017), ɗaliban soja da ke ƙarƙashin tallafi suna da haƙƙin samun RCA a kowace rana.
Sojojin da abin ya shafa sun bayyana cewa rashin biyan su alawus ɗin ya nuna halin ko-in-kula da mahukuntan sojoji ke yi wa sadaukarwar da suke yi wa ƙasa.
Sun ƙara da cewa wannan yanayin yana sa su cikin yunwa tare da rage musu ƙarfin guiwa.
“Mu ɗaliban Makarantar Sojojin Najeriya (NASI) da ke Jaji, Jihar Kaduna, muna sake roƙon mahukuntan soja game da rashin biyan kuɗin alawus ɗinmu na karatu da RCA,” in ji ɗaya daga cikin sojojin.
NASI ita ce babbar makarantar horar da sojoji a yammacin Afirka, wadda aka kafa tun shekarar 1956, mai alhakin koyar da sojojin yaki da hafsoshi dabaru, ƙwarewar yaƙi, da jagoranci.
Manufar makarantar ita ce samar da sojojin yaki da hafsoshin da za su iya yin aiki da kwarewa a cikin yanayi daban-daban da wurare.