Sojojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 a Taraba, Sun Kuma Kwace Makamai

Dakarun musamman na rundunar Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun kashe ƴan bindiga uku tare da lalata sansaninsu a ƙaramar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba.
Wannan nasara ta samu ne ranar 5 ga Afrilu, kamar yadda mai magana da yawun rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana cikin wata sanarwa.
A cewar sanarwar, da sojojin suka isa yankin Chibi, ƴan bindigar suka yi yunkurin tserewa, amma dakarun suka bi sahunsu har suka yi musayar wuta da su.
A yayin hakan, an kashe uku daga cikin su, sannan aka lalata maboyarsu tare da kwato makamai.
Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun sun gudanar da wasu sintiri a baya-bayan nan a yankunan Dutsen Zaki da Achalle, inda suka tarwatsa wasu mazaunan ƴan bindiga a can ma.