December 7, 2025

Sojojin Najeriya sun hallaka ƴan ta’adda da dama a Zamfara

image_editor_output_image-2027153296-1712757048669.jpg

Abdulrazak Namadi Liman

Rahotannin da ke fitowa daga Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga da dama.

Sannan sun kama da dama a raye yayin da mutane 35 suka tsere daga hannunsu.

Jaridar Zagazola Makama ta ruwaito cewa, sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan bindiga da dama tare da samun nasarar kubutar da mutane kusan 35 da aka yi garkuwa da su, a ci gaba da kutsawa cikin sansanonin Yellow Jambros da ke kauyen Dangurgu a karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Wata majiyar leken asiri ta shaida cewa sojojin sun kai samame tare da samun nasarar kawar da wasu sansanonin Dansadau, Maitukunya, Babban Doma da Dangurgu daga hannun ‘yan ta’addar.

Wadanda aka kama dai sun yi nasarar tserewa daga hannun ƴa bindigar ne yayin da suka ranci na-kare a lokacin musayar wuta da sojojin.

Bayanai sun ce Jambros ya tsere ya nufi hanyar Sabon Garin Munhaye, inda yake boye a sansanin Dogo Gide.