Sojojin Najeriya na ƙorafin rashin biyan su alawus-alawus
Daga Sabiu Abdullahi
Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke ayyukan samar da tsaro a jihar Zamfara sun yi korafi game da yawan jinkirin da ake samu, wajen biyansu alawus-alawus, inda suka ce akan biya su kudin wata guda ne kacal bayan kwashe watanni biyu ko uku.
A cewarsu, wannan lamarin yakan jefa su cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
Amma hukumomin sojan Najeriyar sun ce suna sane da wannan kalubale da ke gaban dakarun da ke fagen daga, amma ana hoɓɓasa wajen shawo kan lamarin nan ba da dadewa ba.
Wasu sojojin da suke aiki karkashin rundunar Operation Hadarin Daji a jihar ta Zamfara.
Sun bayar da misali da cewa, sai a ranar Litinin ta wannan mako aka fara biyansu alawus na watan Mayun da ya gabata.
Sannan sun nuna fargabar cewa mai yiwuwa kafin a biya su alawus na watan Yuni sai cikin watan Satumba mai zuwa.
Sun ce akwai ma wadanda daga cikinsu har yanzu ba a ma biya su alawus na watan Maris ba.
Sojojin da ke fagen dagar sun bara, cewa tsaikon biyansu alawus na jefa su cikin tsaka-mai-wuya.
Sai da da BBC Hausa ta tambaye shi, Guruf Kyaftin Ibrahim Ali Bukar, mataimakin daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron Najeriyar, yaba da irin ƙoƙarin da dukkan jami’ansu suke yi wajen yaki da ƴan’ta’adda.
Sannan ya ce: “Shugaban sojoji Janar Christopher Musa, zai yi duk abin da zai yuwu domin ganin an kyautata masu, kuma su ci gaba da samun nasarori a daƙile ƴan ta’adda, dangane da matsaloli da ake fuskanta, ana kan yin abin da ya dace, da zaran babban bankin Najeriya ya kammala aikinsa kowa zai samu abinshi, Insha Allah.”
Guruf Kyaftin Ibrahim Ali Bukar ya ce Janar Christopher Musa ya yi kwamandan yaƙi saboda haka ya san dukkan matsalolin da ke tattare da soja a daji, “Kowa zai samu kudinsa kai tsaye ta asusun bankinsa saboda haka ake yi.”