May 17, 2025

Sojojin Indiya Da Na Pakistan Sun Sake Musayar Wuta a Kan Iyakar Kashmir

India_Kashmir_Attack_29792-70783c7f1617582a953f01a231613630-1745639631264

Sojojin ƙasashen Indiya da Pakistan sun sake musayar harbe-harbe a daren jiya, a kan layin raba iyaka da ke yankin Kashmir da ake taƙaddama a kai, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.

AFP ta ce ta samo bayanan daga wata sanarwa da rundunar sojin Indiya ta fitar, inda ta bayyana cewa sojojin Pakistan sun fara bude wuta “ba tare da wani dalili ba” daga wurare daban-daban da ke kan iyakar Kashmir.

“Sojojin Indiya sun mayar da martani yadda ya kamata da ƙananan makamai,” in ji sanarwar rundunar.

Sai dai sanarwar ta kara da cewa babu wani rahoton da ya nuna asarar rai a lokacin musayar wutar.

Wannan dai shi ne karo na biyu a jere da ake samun irin wannan musayar harbe-harbe tsakanin kasashen biyu a yankin da ake fama da rikice-rikice tsakanin bangarorin soji.