Sojoji sun yi luguden wuta wa ƴan bindiga inda suka hallaka sama da 100 a Zamfara
Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji (OPHD) ta kai farmaki ta sama a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, inda aka ce ‘yan bindiga sama da 100 ne suka mutu.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya dakile shirin da ‘yan bindigar suka yi na kai wa kauyukan jihar Kebbi hari.
Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa ‘yan bindigar da ba a tantamce adadinsu na, dubunsu ta cika ne a ranar Talata a lokacin da suke yunkurin yin kaura daga dajin jihar Zamfara zuwa jihar Kebbi.
Da samun labarin kasancewar sojojin Najeriya a kan hanyarsu sai ‘yan bindigar suka koma yankin Dansadau na karamar hukumar Maru.
An dauki matakin gaggawa, yayin da rundunar sojojin saman Najeriya ta fatattaki ‘yan bindigar tare da kashe sama da 100 daga cikinsu tare da lalata baburansu.
Wasu da dama sun samu raunuka. An binne gawarwakin ‘yan ta’addan da aka kashe a wani ƙaton rami a dajin Sangeko da ke Jihar Neja da Babban Doka da ke karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.
Kaftin Yahaya Ibrahim, mai magana da yawun rundunar Operation Hadarin Daji, ya tabbatar da harin ta sama, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.
Air Commodore Edward Gabkwet, daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojojin saman Najeriya (DOPRI) ya tabbatar da harin amma ya ƙi bayyana haƙiƙanin adadin waɗanda suka mutu.
Jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa irin su Neja, Kaduna, Sokoto, Kebbi, Katsina, na shan fama da matsalar ‘yan fashi da makami.