January 15, 2025

Sojoji sun sha alwashin kama madugun ƴan bindiga Bello Turji

30
images (11) (1)

Daga Sabiu Abdullahi  

Rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin kama Bello Turji, ɗanbindigar da ya shahara wajen addabar jihar Zamfara da wasu sassan Arewa maso Yamma.  

“Mun kuduri aniyar kawo karshen harajin da Turji da sauran ‘yan ta’adda ke dorawa manoma,” Inji Janar Christopher Musa, Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Najeriya yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar tsaro da ke Abuja.

“Kwanakin shugaban ‘yan fashin sun yi kusa ƙarewa, don haka muna kira ga ‘yan kasa da su ba da goyon baya ga kokarinmu na maido da zaman lafiya.”

Janar Musa ya bayyana cewa duk da yunkurin ‘yan fashin na kawo cikas ga rayuwar manoma, sojoji suna bakin kokarinsu wajen kawo karshen wadannan ta’asa.  

Ya kuma gargadi al’umma da su guji ba da goyon baya ko kuma ba da bayanai ga ‘yan ta’addan, yana mai cewa, yin hakan yana kara tsawaita rikicin.

30 thoughts on “Sojoji sun sha alwashin kama madugun ƴan bindiga Bello Turji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *