January 15, 2025

Sojoji sun kama wasu ƴanta’adda a asibiti yayin da suke jinya a Kaduna

127
IMG-20240928-WA0003

Abdulrazak Namadi Liman

A wani samame da jami’an tsaro suka yi a Kaduna sun samu nasarar cafke wasu ‘yanta’adda guda biyu da suke jinya a wata asibiti mai zaman kanta da ke Jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda ake zargin sun tsere zuwa asibitin ne bayan da suka samu raunuka a wani harin da sojoji suka kai musu a wata arangama da suka yi a kwanakin baya baya.

Ƴanta’addan sun nemi kulawar lafiya bayan sun tsere daga harin da sojoji suka kai musu.

Bayan samun bayanan sirri, daga nan sai sojoji suka shiga cikin gaggawa, inda suka kama wadanda ake zargin ba tare da turjiya ba.

127 thoughts on “Sojoji sun kama wasu ƴanta’adda a asibiti yayin da suke jinya a Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *