Sojoji sun fatattaki ƴan bindiga a Sokoto
Rahotanni da ke fitowa daga jihar Sokoto na nuna cewa, wata tawagar Jami’an tsaron Soji haɗin gwiwa da ƴan sa-kai a yankin ƙaramar hukumar Sabon-birni sun bazama daji domin fatattakar ƴan-bindiga.



Bugu da ƙari, jami’an tsaron sun tarwatsa duk wani sansani da maɓoyar ƴan-ta’adda da ke daji ta janyar ƙone dajin
Saidai zuwa yanzu ba a tabbatar da lamarin ba a hukumance.

Ƙoƙarin TCR Hausa na samun wani bayani daga hukumomi game da lamarin ya ci tura.
Jihar ta Sokoto dai tana ɗaya daga cikin jihohi Arewa maso Yamma da ƴan bindiga suka addaba a kwanakin nan.






