January 24, 2025

Shugabannin Arewa da Suka Nuna Rashin Amincewarsu Ga Sabon Ƙudurin Dokar Haraji

1
1733137034.jpeg


Daga Sabiu Abdullahi
 
Tattaunawa mai zafi ta kunno kai a Najeriya kan kudirin dokar gyaran haraji da Gwamnatin Tarayya ke kokarin gabatarwa karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
 
Duk da haka, wasu manyan shugabannin Arewa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum, da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Tambuwal, sun nuna damuwarsu kan tasirin wannan kudiri ga tattalin arzikin yankin Arewa.
 
Shugabannin na Arewan sun nuna tsoron cewa wadannan gyare-gyare na haraji za su fi shafar jihohin Arewa, wanda hakan zai kara zurfafa bambance-bambancen tattalin arziki tsakanin kudancin Najeriya mai arziki da Arewa mai rauni.
 
Atiku Abubakar ya jaddada bukatar a yi adalci da bayyananniyar manufa yayin duba wannan kudiri a Majalisar Tarayya.
 
“Yan Najeriya sun hade wuri guda wajen neman tsarin haraji da ke tabbatar da adalci da daidaito,” in ji shi.
 
Haka zalika, Babagana Zulum ya soki yadda ake hanzarta wannan kudiri a Majalisar Dokoki, inda ya kwatanta hakan da kudirin dokar masana’antar man fetur (PIB) wanda aka dauki tsawon kusan shekaru ashirin kafin a yi shi.
 
“Me ya sa hanzarin?” ya tambaya. “Ya kamata a yi masa nazari a hankali don ko bayan mu, ya amfanar da ‘ya’yanmu.”
 
Idan ba a manta ba, Majalisar Wakilai ta dakatar da muhawara kan kudirin harajin har sai abin da hali ya yi, sakamakon matsin lamba daga gwamnonin Arewa da ‘yan majalisar Arewa su 73.
 
Sai dai shugabannin Arewa suna da ra’ayi cewa wadannan dokoki za su yi mummunan tasiri ga yankin Arewa da sauran sassan kasar.
 
Wani jigo daga Arewa da ya yi karfi wajen nuna adawarsa da kudirin shi ne Sanata Ali Ndume daga Borno.
 
A cewarsa, babu dalilin wannan gaggawar, ganin cewa har yanzu akwai abubuwa da dama game da kudirin da ba a bayyana ba, kuma ya kamata a yi sauraron ra’ayoyin jama’a kafin amincewa da shi.
 

1 thought on “Shugabannin Arewa da Suka Nuna Rashin Amincewarsu Ga Sabon Ƙudurin Dokar Haraji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *