March 28, 2025

Shugaban Syria Ya Caccaki Trump Kan Batun Falasɗinawa

26c3b65b-93a8-489c-b7cd-5111c5ecb178.jpg.webp

Shugaban ƙasar Syria, Ahmed al-Sharaa, ya bayyana cewa Donald Trump ya samu dama ta “fara zangonsa na biyu” a wata hira da aka yi da shi.

Shugaban na Syria ya yi kira ga Trump da ya janye duk wasu takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria, yana mai cewa yanzu gwamnatin ƙasar ta sauya.

Sai dai harshensa ya canza lokacin da aka tambaye shi ra’ayinsa kan batun kwashe Falasɗinawa daga Gaza.

Al-Sharaa ya ce, “Babu wani dalili na hankali ko na shari’a da ke bai wa Trump damar jagorantar sauya wa Falasɗinawa matsuguni zuwa wata ƙasa da ba tasu ba.”

Ya kuma ƙara da cewa wannan yunƙuri “babban laifi ne wanda ba zai samu nasara ba a ƙarshe.”

1 thought on “Shugaban Syria Ya Caccaki Trump Kan Batun Falasɗinawa

Comments are closed.