Shugaban Iran Ya Sallami Mataimakinsa Saboda Tafiya Shaƙatawa Yayin Tsadar Rayuwa

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya kori ɗaya daga cikin mataimakansa, Shahram Dabiri, saboda wata tafiya shaƙatawa da ya yi zuwa Antarctica tare da matarsa a lokacin hutun Nowruz.
A cikin wata sanarwa, ofishin shugaban ƙasar ya bayyana tafiyar a matsayin “wata hanya ta almubazzaranci” da bai dace ba, musamman a lokacin da ƙasar ke fama da matsanancin hali na tattalin arziƙi.
Hotunan Dabiri da matarsa suna jin daɗi a tafiyar sun karade kafafen sada zumunta, inda suka haifar da ƙorafe-ƙorafe daga jama’a.
Shugaba Pezeshkian ya ce ya yanke hukuncin sallamar Dabiri daga mukaminsa na mataimakin shugaban ƙasa mai kula da al’amuran majalisa, duk da cewa Dabiri ne ya biya kuɗin tafiyar daga aljihunsa.
“Wannan gwamnatin na bin koyarwar Imam Ali, kuma ba zai dace wani jami’in gwamnati ya tafi wata tafiyar da za a kashe maƙudan kuɗi ba – ko da kuwa daga kuɗin kansa ne,” in ji shugaban.