Shugaban Ghana Mahama ya dakatar da Babbar Alƙaliya Torkornoo

Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya dakatar da Babbar Alƙaliya ta ƙasar, Mai Shari’a Gertrude Torkornoo, a wani mataki da ya kasance irinsa na farko a tarihin Ghana.
Mahama ya kuma bayar da umarni da a gudanar da bincike a kanta, sakamakon ƙorafe-ƙorafe uku da aka shigar, ko da yake ba a bayyana ainihin abin da ƙorafe-ƙorafen suka ƙunsa ba.
A cewar kundin tsarin mulkin Ghana, ba za a iya sauke Alƙalin Alƙalai daga muƙaminsa kai tsaye ba sai idan an tabbatar da shi da laifin rashin ƙwarewa ko karya doka.
Wannan ya sa wasu ke kallon dakatarwar a matsayin yunƙurin shisshigi ga harkokin shari’a na ƙasar.
A watan da ya gabata ne Shugaba Mahama ya mika ƙorafe-ƙorafen da ke neman sauke Mai Shari’a Torkornoo ga Majalisar Magabata, domin ta duba lamarin bisa tanadin kundin tsarin mulki.
Rahotanni daga Kamfanin Dillancin Labaran Ghana sun ce wannan mataki wani ɓangare ne na bin ka’idar sauke Alƙalin Alƙalai da Layi na 146 na Kundin Tsarin Mulkin ƙasar na 1992 ya tanada.