June 14, 2025

Shugaban Chadi Ya Haramta Bada Visa Ga ‘Yan Asalin Amurka

0
images (35)

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Itno, ya bayar da umarnin dakatar da bayar da visa ga ‘yan ƙasar Amurka, a matsayin martani ga haramcin tafiye-tafiye da gwamnatin Amurka ta sanya wa ƙasarsa.

Chadi, ƙasa dake tsakiyar nahiyar Afirka, na daga cikin ƙasashe 12 da tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya saka cikin jerin ƙasashen da aka kakabawa haramcin tafiye-tafiye, yana mai cewa matakin na da nufin kare tsaron ƙasarsa.

Shugaban Chadi ya bayyana matakin nasa a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, inda ya ce ya umarci gwamnati da ta bi tsarin daidaituwar aiki ta hanyar dakatar da bayar da visa ga Amurkawa.

“Na umurci gwamnati da ta bi ƙa’idar musayar aiki da ta dakatar da bayar da visa ga ‘yan ƙasar Amurka,” in ji Itno.

Matakin na Itno na zuwa ne bayan jinkirin da aka samu na tsawon lokaci tun bayan kakabawa Chadi takunkumin shiga Amurka, lamarin da ya jawo suka daga cikin ‘yan kasar Chadi da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *