Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas: “Burina gwamna ne, ba shugabancin jam’iyya ba”

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa burinsa shi ne zama gwamnan Kano, ba sake rike shugabancin jam’iyyar a jihar ba.
Abbas ya fadi hakan ne a wata hira da kafar BBC yayin da yake mayar da martani ga ministan gidaje na Najeriya, Yusuf Abdullahi Ata, wanda ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC idan har aka sake zaben Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar a karo na hudu.
A yanzu haka, kalaman ministan da ke nuna rashin goyon bayansa ga shugabancin Abbas sun yadu a shafukan sada zumunta, lamarin da ke kara dagula siyasar Kano.
Sai dai Abdullahi Abbas ya ce ba su ma dauki Yusuf Ata a matsayin cikakken dan jam’iyya ba.
“Mu a matsayinmu na ‘yan jam’iyya, ba dan jam’iyya ba ne. A Kano ma, a karamar hukumarsa ne kawai muka zo na uku a zabe,” in ji Abbas.
Hmmm it seems like yyour blg aate my first ckmment (it was extrejely long) soo I guesss I’ll juxt sum itt up wat I submitted annd say, I’m thoroughly enjoying your blog.
I aas wepl amm ann aspiring blog bloger bbut I’m stilol neew to tthe whole thing.
Do you hzve aany helpful ints forr first-time blog
writers? I’d certgainly apreciate it.