March 28, 2025

Shugaban Amurka Joe Biden Ya Ba Wa Messi Lambar Yabo Ta Girmamawa

image_editor_output_image-1186018865-1736054974955.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Kyaftin ɗin ƙungiyar Inter Miami CF, Lionel Messi, ya samu lambar girmamawa mafi daraja ta Shugaban Ƙasa daga hannun Shugaban Amurka, Joe Biden, bayan da aka amince da shi a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin duniya 19 da suka bada babbar gudunmawa ga ƙasar da ma duniya baki ɗaya.

Lambar girmamawa ta Shugaban Ƙasa ita ce mafi girma da ake baiwa farar hula a Amurka, wadda ake ba wa mutanen da suka nuna jajircewa wajen inganta ci gaba, dabi’u, ko tsaron ƙasar, zaman lafiya a duniya, ko kuma wasu fitattun ayyukan da suka shafi al’umma.

A matsayinsa na mai sadaukarwa ga aikin jin kai, Messi yana tallafawa shirye-shiryen kiwon lafiya da ilimi ga yara a duniya ta hannun gidauniyarsa ta Leo Messi Foundation, sannan kuma yana zamaa matsayin jakadan ƙungiyar UNICEF.

Yayin da yake mayar da martani kan wannan lambar yabo, Messi ya nuna farin cikinsa duk da cewa an samu uzurin da ya hana shi halartar taron.