Shugaba Tinubu Zai Ziyarci Faransa Kafin Halartar Taron AU a Habasha

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Laraba don wata ziyarar zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa, kafin ya wuce zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha.
A Addis Ababa, Shugaba Tinubu zai halarci taron shugabannin Afirka a zama na 46 na majalisar zartarwa da kuma zama na 38 na shugabannin ƙasashen kungiyar Tarayyar Afirka (AU), wanda zai gudana daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabrairu, 2025.
Ana sa ran shugaba Tinubu zai isa Addis Ababa a farkon mako mai zuwa domin halartar taron koli na Tarayyar Afirka.
A yayin ziyararsa a Faransa, Shugaba Tinubu zai gana da takwaransa na ƙasar, Shugaba Emmanuel Macron.
q2okiy
Hi there i am kavin, its myy first time to ommenting
anywhere, when i rerad this piece of writing i thought i could
aso create comment duue too this brilliant article.