Shugaba Tinubu zai rage jiragen fadarsa saboda irin kuɗaɗen da suke laƙumewa
Daga Sabiu Abdullahi
Za a sayar da jiragen sama guda uku a cikin jerangiyar jiragen Shugaban Kasa a Najeriya don rage yawan kuɗin tafiyar da gwamnati.
A cewar jaridar The Nation, akwai jirage 10 a halin yanzu a cikin jiragen shugaban kasar – jet shida da jirage masu saukar ungulu hudu – wadanda za a yanke su zuwa bakwai idan shirin da aka tsara ya kai ga gaci.
A cewar rahoton, wannan wani bangare ne na matakan ceton tattalin arziki da ke cikin shirin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Kasafin Naira Biliyan 80 ne aka ware wa jiragen a matsayin kudin kulawa, daga 2016 zuwa 2023.
A shekarar 2016 (N3.65bn), 2017 (N4.37 billion), 2018 (N7.26 billion), 2019 (N7.30) biliyan), 2020 (N6.79 biliyan), 2021 (N12.55 biliyan), 2022 (N12.48 biliyan) da kuma a 2023 kimanin N25.7billion, wanda ya kai naira biliyan 13 a cikin kasafin kudi da kuma N12.7billion a cikin Karin Kasafin 2023.




