June 14, 2025

Shugaba Tinubu Zai Lula Ghana Don Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Ƙasa

images-85.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai tafi Ghana a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu, domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, da za a gudanar ranar Talata, 7 ga Janairu.

Wannan zai zama bulaguronsa na farko zuwa wata ƙasa a shekarar 2025.

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, an bayyana cewa Tinubu zai halarci bikin ne bisa gayyatar da sabon shugaban ƙasar ya yi masa, bayan ziyarar da Mahama ya kai masa a Najeriya cikin watan Disamba.

“Tinubu da Mahama na da kyakkyawar abota mai tsawo, kamar yadda Najeriya da Ghana suka jima suna da dangantaka mai ƙarfi,” in ji sanarwar.

3 thoughts on “Shugaba Tinubu Zai Lula Ghana Don Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Ƙasa

  1. Fantastic beat I would like to apprentice while you amend your web site how could i subscribe for a blog site The account helped me a acceptable deal I had been a little bit acquainted of this your broadcast offered bright clear conceptHABANERO88

Comments are closed.