June 14, 2025

Shugaba Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Dr Idris Abdulaziz

images - 2025-04-04T214336.462

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu da safiyar ranar Juma’a yana da shekara 68.

A cikin saƙonsa na ta’aziyya, Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora wanda ya ilmantar da matasa da dimbin Musulmi kan koyarwar addinin Musulunci.

Shugaban ya ce Dr Abdulaziz ya taka muhimmiyar rawa wajen dakile tasirin ra’ayoyin masu tsattsauran ra’ayi, musamman a farkon rikicin Boko Haram.

Ya kuma bayyana cewa Musulmai za su yi matuƙar rashin muryar marigayin da kullum ke kira da a zauna da gaskiya da rikon amana.

A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan Dr Abdulaziz tare da ƙarfafa iyalansa da mabiyansa da su samu kwanciyar hankali da jin daɗin irin ayyukan alherin da ya bari.