January 15, 2025

Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin kammala aikin titin jirgin kasa na Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano  

0
FB_IMG_1720723074529

Daga Sabiu Abdullahi  

Shugaba Bola Tinubu ya bada tabbacin kammala aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano domin amfanar da Najeriya da yammacin Afrika.  

A yayin ziyarar da ya kai hedkwatar kamfanin samar da layin dogo na kasar Sin (CRCC) da ke birnin Beijing, Tinubu ya amince da rawar da CRCC ke takawa a matsayin amintaccen abokin hadin gwiwa wajen samar da ababen more rayuwa a Najeriya.  

“Hakazalika yana da matukar muhimmanci mu ba wa al’ummar Najeriya tabbacin a fadin yankunanmu cewa za a kammala aikin titin jirgin kasa daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano da kuma yinsa yadda zai amfanar da Najeriya da Afrika ta Yamma baki daya,” inji Tinubu.  

Shugaban CRCC Dai Hegen ya bayyana cewa kamfanin ya shafe shekaru 43 yana aiki a Najeriya, inda ya aiwatar da ayyuka sama da 300 tare da horar da ma’aikatan gida 100,000.  

Ya nuna cewa titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da Legas zuwa Ibadan sun yi jigilar fasinjoji kusan miliyan 9 da tan 180 na kaya.  

Bugu da kari, shugaba Tinubu ya ziyarci cibiyar bincike ta Huawei Technologies’s Beijing, inda kamfanin ya kaddamar da DigiTruck, ajujuwan ICT ta wayar tafi da gidanka da nufin bunkasa ilimin yanar gizo a cikin al’ummomin Najeriya.

Kamfanin Huawei ya sanar da shirin yin aiki a jihohi 10 a duk shekara, inda zai horar da dalibai akalla 3,000 kowace shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *