December 7, 2025

Shugaba Tinubu Ya Sake Naɗa Marwa A Matsayin Shugaban NDLEA

1763114951499

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da sake naɗa Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (rtd) a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na tsawon wasu shekaru biyar.

Bayo Onanuga, Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Bayanai da Tsara Dabaru, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar 14 ga Nuwamba, 2025.

An fara naɗa Marwa ne a watan Janairun 2021 karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Kafin wannan lokaci, ya jagoranci Kwamitin Shugaban Kasa na Yaki da Sha da Miyagun Kwayoyi daga 2018 zuwa Disambar 2020.

Sabon wa’adin ya nuna zai ci gaba da jagorantar NDLEA har zuwa shekarar 2031.Marwa, dan asalin jihar Adamawa, ya rike mukamai da dama a rundunar soji da sauran ofisoshin gwamnati. Ya yi mulkin soji a jihohin Legas da Borno.

Ya kammala karatu a Nigerian Military School da kuma Nigerian Defence Academy.Tun bayan saukarsa karagar soji a 1973 a matsayin second lieutenant, ya yi aiki a matsayin brigade major na 23 Armoured Brigade.

Ya kuma kasance ADC ga tsohon Chief of Army Staff, Laftanar-Janar Theophilus Danjuma. Baya ga haka, ya yi aiki a matsayin academic registrar na NDA, sannan ya yi aiki a ofishin jakadancin Najeriya a Washington DC da kuma Majalisar Dinkin Duniya a matsayin mai ba da shawarar tsaro.

Marwa ya mallaki digirori biyu na gaba da digiri na farko daga kasashen waje.

A lokacin da yake jagorantar NDLEA, hukumar ta yi manyan samame, ciki har da kama fiye da mutane 73,000 da ake zargi a matsayin masu safarar miyagun kwayoyi, tare da kwace sama da kilo miliyan 15 na kwayoyi iri-iri.

Hakanan NDLEA ta fadada yaƙi da matsalar shaye-shaye a fadin kasar.