Shugaba Tinubu ya miƙa wa Gwamnan Akwa Ibom ta’aziyya bisa rasuwar uwargidansa
Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, bayan rasuwar mai dakinsa Fasto Patience Umo Eno.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya jajanta wa iyalan Eno, gwamnati, da al’ummar jihar Akwa Ibom a wannan lokaci na baƙin ciki.
Tinubu ya yabawa uwargidan gwamnan, inda ya nuna goyon bayanta ga gwamnatin Gwamna Eno.
“Patience Eno, a matsayin matar gwamna mai hangen nesa kuma mai hidimar bushara, tana da tawali’u, juriya, da aminci,” in ji shi.