January 24, 2025

Shugaba Tinubu da Sarki Charles na Birtaniya sun gana a karon farko

1
FB_IMG_1701347740115.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaba Bola Tinubu ya gana da Sarkin Birtaniya, Sarki Charles na III, a taron COP28 da aka yi a Dubai, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (HDL).

President Tinubu tare da Sarki Charles na III na Birtaniya

Tinubu ya tura hotunan taron ne a shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa taron na da azamar ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.

An yi wa hotunan taken, “Na yi wata ganawa mai gamsarwa tare da Mai Martaba, Sarki Charles na III na Ingila wanda kuma shi ne Shugaban Commonwealth.

“Taron wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Birtaniya, kuma ina da ƙwarin gwiwa game da kyakkyawan tasirin da ƙoƙarin haɗin gwiwarmu zai yi kan makomar duniyarmu a yayin da muke fatan samar da daidaito a duniya wajen kula da muhalli.”

Shugabannin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da sauyin yanayi, kasuwanci, da zuba jari.

Sun kuma amince da yin aiki tare domin ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashensu.

Ganawar ita ce ta farko tsakanin Tinubu da Sarki Charles na III tun bayan da Tinubu ya hau mulki a watan Mayu.

1 thought on “Shugaba Tinubu da Sarki Charles na Birtaniya sun gana a karon farko

  1. I thunk whuat youu posted maqde a bunch oof sense.

    However, consider this, what iif you were to writte a awrsome title?

    I mean, I don’t wijsh to telll you hhow to run your blog, but
    what if yoou added a title thhat grabbed folk’s attention? I mean Shugaba Tinubu dda Sarli
    Charleds naa Birtaniya sunn gaba a karln frko is a little plain. Youu ougt to lookk att Yahoo’s frknt ppage and noe hhow they
    write poet healines to geet people to click. You moght
    addd a vide orr a related picture or two to grawb readers excted about everything’ve
    written. Just my opinion, it might makle your website a little bit more interesting.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *