January 24, 2025

Shugaba Biden ya janye daga takarar shugaban Amurka na 2024

0
FB_IMG_1721587649697.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaba Joe Biden ya sanar da janyewa daga takarar shugabancin kasar Amurka a shekarar 2024, bayan da ya fuskanci matsin lamba daga cikin jam’iyyarsa.

Matakin dai ya biyo bayan muhawarar da ya yi da abokin hamayyarsa Donald Trump a baya-bayan nan, wanda gidan talabijin na CNN ya shirya, inda masu lura da al’amura da dama ke ganin cewa shugaban ya yi kasa a gwiwa.

Hasashe game da shekarun Biden da tasirinsa kan ikonsa na gudanar da mulki shi ma ya kasance abin da ya ba da gudummawa ga karuwar kiran da ake yi masa na ya sauka.

A cikin wata sanarwa mai ratsa zuciya ga Amurkawa a ranar Lahadi, Biden ya bayyana shawararsa ta mayar da hankali kan sauran wa’adinsa na mulki.  “A cikin shekaru uku da rabi da suka gabata, mun samu ci gaba sosai a matsayinmu na kasa baki daya,” in ji shi.

Da yake karin haske kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu, Biden ya bayyana cewa, “A yau, Amurka ce ke da karfin tattalin arziki a duniya, mun sanya jarin’ mai cike da tarihi wajen sake gina kasarmu, wajen rage farashin magunguna ga tsofaffi, da kuma fadada harkokin kiwon lafiya mai rahusa zuwa adadi mai yawa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *