Shirin zuwa Hajji da Gwamnan Osun ke yi ya ta da ƙura kan addininsa
Daga Sodiqat Aisha Umar
Shirin zuwa Hajji da Gwamnan Osun ke yi ya ta da taƙaddama saboda addininsa.
Har zuwa yau al’ummomin Jihar Osun sun kasa gano ainihin addinin da Gwamnan Jihar, Mista Ademola Nurudeen Jackson Adeleke yake bi.
Hakan ya biyo bayan yawan ganin Gwamnan ne a masallaci da coci yana bauta kamar yadda mabiya addinin Musulunci da Kiristanci suke yi wanda hakan ke ci-gaba da janyo cece-ku ce a cike da wajen jihar.
Sai dai Sarkin Hausawan Ede kuma Sakataren Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihar Osun ya bayyana cewa, duk wanda yake zaune a garin Ede wato asalin garin su gwamnan ya san cewa Gwamna Ademola Adeleke da babban yayansa tsohon Gwamnan Jihar Osun marigayi Isyaka Adeleke da sauran ’yan uwansu an haife su ne a Musulunci.