Shin Me Ya Haifar da Gaba Tsakanin India da Pakistan?

Gaba tsakanin ƙasashen India da Pakistan ba sabon abu ba ne, domin tun kafin su sami ‘yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1947, an riga an samu sabani da rashin jituwa da ta haifar da rikice-rikice da dama, musamman kan yankin Kashmir.
Asalin Matsalar
A shekarar 1947, lokacin da Birtaniya ta janye daga yankin kudu maso Asiya, an raba India gida biyu — India mai rinjayen Hindu da Pakistan mai rinjayen Musulmi. Wannan rabuwar ta zo da bala’i, inda mutane sama da miliyan 10 suka tsere daga gidajensu, kuma sama da mutum miliyan daya suka rasa rayukansu a rikice-rikicen kabilanci da na addini.
Batun Kashmir
Bayan rabuwar, an bar wasu yankuna da za su zaɓi shiga kowace ƙasa. Wani daga cikin waɗannan yankuna shi ne Jammu da Kashmir — wanda ke da yawancin Musulmi, amma sarkin yankin Hindu ne.
Sarkin ya yanke shawarar haɗewa da India, abin da Pakistan ba ta amince da shi ba. Wannan ne ya tayar da rikici, inda aka yi yaƙi na farko tsakanin ƙasashen a shekarar 1947–1948.
Rikicin Kashmir ya ci gaba har zuwa yau, inda kowanne daga cikin ƙasashen biyu ke ikirarin mallakar yankin gaba ɗaya.
An sha shawarwari da sulhu, amma babu wanda ya haifar da dawwamammen zaman lafiya.
Yaƙe-yaƙe da Rikice-rikice
India da Pakistan sun yi yaƙi sau uku — a 1947, 1965, da 1971 — kuma duk suna da alaƙa da Kashmir ko siyasar yankin.
A 1999 ma, sun sake samun rikici a Kargil, bayan dakarun Pakistan sun tsallaka iyaka.
Baya ga yaƙe-yaƙe, an sha kai hare-hare da zargin juna. India ta zargi Pakistan da tallafa wa ‘yan ta’addan Kashmir da ke kai hari a India, yayin da Pakistan ke zargin India da cin zarafin Musulmin Kashmir.
Makaman Nukiliya da Tsoro
A shekarar 1998, India da Pakistan sun gwada makaman nukiliya, abin da ya kara tayar da hankali a duniya. Tun daga lokacin, kowacce ƙasa na nuna damuwa kan yiwuwar rikici ya ɓarke da zai kai ga amfani da makaman kare dangi.
Kwanan Nan
Sabon harin da aka kai a Pahalgam na jihar Jammu da Kashmir inda mutane 26 suka mutu ya sake tayar da jijiyar wuya. India ta zargi ‘yan ta’adda da ke da alaƙa da Pakistan, abin da ya sa ta kaddamar da hare-hare a ƙasashen makwabta. Pakistan ta bayyana matakin a matsayin “harin yaki.”
Gaba tsakanin India da Pakistan na da tushe mai zurfi, wanda ke tattare da tarihi, addini, siyasa da kuma rikicin yankin Kashmir. Har sai an samu maslaha ta gaskiya da amincewa daga ɓangarorin biyu, al’ummar yankin za su ci gaba da rayuwa cikin fargaba da barazana.