January 15, 2025

Shekarau ya buƙaci Tinubu ya rage yawan hadimai da mutanen da ya naɗa a gwamnatinsa

0
image_editor_output_image-453183575-1704881414258.webp

Daga Sabiu Abdullahi

Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya rage yawan wadanda ya nada domin rage yawan kudin da ake kashewa harkar gwamnati.

Shekarau ya yi wannan kiran ne a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels a ranar Talata.

Ya ce, “Wani abin da nake da nake sa rai a yanzu shi ne ya kamata shugaban kasa ya rage yawan mutanen da ke rike da mukamai. Wasu daga cikin waɗannan da aka nada ƙila ba lallai ne a ce ana matukar bukatar aikinsu ba.”

Sai dai, Shekarau ya yaba wa Shugaba Tinubu kan dakatar da ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu.

Rahotanni sun nuna cewa Tinubu, a ranar Litinin, ya umarci Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, Ola Olukoyede, da ya binciki duk wata hada-hadar kudi da ta shafi ma’aikatar Agaji da Rage Talauci ta Tarayya.

Edu ta fuskanci suka ne bayan wata takarda da aka fallasa a ranar 20 ga Disamba, 2023, wadda ta bayyana cewa ta umurci Akanta-Janar na Tarayya, Oluwatoyin Madein, da ya tura naira miliyan 585 zuwa wani asusu mai zaman kansa mallakin wani Oniyelu Bridget.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *