February 10, 2025

Sheikh Ɗahiru Bauchi Ya Nemi Afuwar Al’ummar Musulmi

327
360081770_245267638291279_745402139674841747_n

A wani babban taro da Ɗariƙa Tijjaniyya ta gudanar a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a jiya Alhamis 13 ga watan Yuli, ya nemi afuwar duk wanda ya yi wa kuskure a al’ummar Musulmi, kuma ya ce shi ma ya yafewa duk wanda ya ɓata masa.

Masu sharhi na ganin hakan a matsayin kyakkyawan abu, ganin yadda shekarun Shehin ke ƙara ja. A shekarun bayan nan dai Shehin Tijjaniyyar ya rage yawan halarta tarukka da gabatar wa’azozi da hira da manema labarai kamar yadda yake yi a baya.

327 thoughts on “Sheikh Ɗahiru Bauchi Ya Nemi Afuwar Al’ummar Musulmi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *