April 19, 2025

Saudiyya Za Ta Hana Shiga Ƙasar Sai Ga Masu Bizar Aikin Hajji Daga 29 Ga Afrilu

0
images - 2025-04-13T110607.747

Gwamnatin Saudiyya ta sanar da cewa daga ranar 29 ga watan Afrilu, ba za a bar kowa ya shiga ƙasar ba sai wanda ke da bizar aikin hajji.

Wannan na daga cikin sabbin ƙa’idojin da aka ƙirƙiro domin gudanar da aikin hajjin bana cikin tsari da kulawa.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Saudiyya ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar dangane da matakan kula da aikin hajji.

Ɗaya daga cikin sabbin matakan ya tanadi cewa ba za a bar ƴan ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje su shiga birnin Makka ba, in har ba su da wani dalili na musamman da ke tabbatar da buƙatar hakan.

Ma’aikatar ta bayyana cewa za a bar waɗanda asalinsu daga birnin Makka ne su shiga, muddin adireshin zamansu na nuna hakan.

Haka zalika, za a ba da damar shiga ga mutanen da aka amince da su don gudanar da aiki a cikin Harami.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Wannan wani muhimmin mataki ne da ke cikin sauye-sauyen da muka shigo da su domin tabbatar da lafiya da tsaro a lokacin aikin hajjin bana.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *