January 14, 2025

Saudiyya Ta Yi wa Mbappe Wani Gwaggwaɓan  Tayin Da Ba a Taɓa Ba A Tarihi

0

Daga Katib AbdulHayyi

Ƙungiyar Al-Hilal ta ƙasar Saudi Arebiya ta yi wa Kylian Mbappe wani wawan tayi mai sa a riƙe baki. Al Hilal ta ayyana Yuro miliyan ɗari uku (kwatankwacin Naira biliyan ɗari biyu da sittin da uku – 263Bn) tare da niyyar ƙarin wata Yuro 200 – kwatankwacin Naira biliyan 175, don ya amince da sa hannu a kwantiragin shekara ɗaya tak.

Tayin ya biyo bayan ajiye ɗan wasan gaban Faransa, ɗan Asalin Kamaru da ƙungiyarsa ta PSG ta yi daga tawagar da za su je Japan don share fagen fafatawar kaka mai zuwa. Hakan alama ce ƙarara ta cewa ƙungiyar ta shirya rabuwa da ɗan wasan, muddin ba su daidai ya tsawaita zamansa da su ba.

Masharhanta na ganin PSG ba za ta yi wata-wata ba wajan sallamawa Al Hilal, sai dai har yanzu Al Hilal da Mbappen ba su tattauna a tsakaninsu ba. Kuma PSG na ganin akalar mai shekara 24 ta fi karkata zuwa Riyal Madarid ta kasar Sifaniya.

Ana ganin dai Al Hilal za ta matsa ƙaimi don ganin ta farauto masanin ragar da maɗuɗun kuɗin da ba a taɓa biyan wani ɗan ƙwallo ba a duniya, da zai kai Yuro miliyan 700 a shekara – fiye da rabin tiriliyan na Naira, idan aka haɗa da albashinsa.

Ko Mbappen zai dage da ƙudurinsa na tafiya Madarar ƙwallo don ci gaba da kafa tarihi da neman ƙarin ɗaukaka, ko kuma dai zai bi almalu masu gida rana a ƙasar Larabawan shayin?

Shawara ta rage wa mai shiga rijiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *