November 8, 2025

Saudiyya Ta Saki Wasu Mata Uku ‘Yan Nijeriya Da Aka Kama Bisa Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi

images-84.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta sanar da sakin wasu mata uku da Saudiyya ta kama a bara bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

Sunayen wadanda aka kama su ne Hadiza Abba, Fatima Umate Malah, da Fatima Kannai Gamboi.

An kama su ne a ranar 5 ga Maris, 2024, a filin jirgin saman Mohammed bin Abdulaziz da ke Madinah.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta fitar a ranar Lahadi ta bayyana cewa an kama matan ne biyo bayan kamun wasu ‘yan Nijeriya biyu da aka samu da kafso 60 na hodar iblis mai nauyin gram 900.28, da kuma kafso 70 mai nauyin gram 789.5.

“Hukumomin Saudiyya sun tsare matan bisa zarginsu da taimakawa wajen safarar kayan haram da aka samu tare da ‘yan Nijeriyan da aka kama,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “An samu nasarar sako matan ne bayan doguwar tattaunawa ta diflomasiyya da shari’a, wanda ya kai ga sallamarsu da wanke su daga zargin. Daga bisani an mika su ga ƙaramar ofishin jakadancin Nijeriya da ke Jedda.”