June 14, 2025

Saudiya Ta Kama Mahaifiya da Matar Ado Aliero Yayin Aikin Hajji

images - 2025-05-20T084857.268

Jami’an tsaro a ƙasar Saudi Arabia sun kama mahaifiya da kuma matar shahararren ɗan ta’adda Ado Aliero, bayan sun isa ƙasar domin gudanar da aikin Hajji.

Rahotanni sun bayyana cewa, kafin kamun, matar Ado Aliero ta wallafa wani faifayin bidiyo a shafinta na Tiktok daga ƙasa mai tsarki, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Kamun na su ya zo ne a daidai lokacin da jami’an tsaro a Najeriya ke samun yabo saboda nasarar da suka samu wajen cafke wasu masu hannu da shuni cikin ta’addanci a filin jirgin sama na Abuja da kuma a jihar Sakkwato, a yayin da ake tantance alhazai masu niyyar sauke farali a Saudiyya.

Sai dai har yanzu hukumomin Saudiyya ba su fitar da cikakken bayani ba kan dalilan kamun nasu.