Sarkin Musulmi ya yaba wa matashin da ya tsinci maƙudan kuɗi kuma ya mayar wa mai shi a Kano
Daga Nura Mudi
Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III Ya karrama matashi Auwal Salisu ɗan Jihar Kano wanda aka manta kudi kimanin naira milliyan 18 ya mayar ga mai kuɗin ɗan kasar Chadi ta hannun Arewa Radiyo.
Wakilinmu Nura Haruna Mudi ya rawaito cewa, sarkin Musulmin ya kuma karrama mahajjaciya ‘yar Jihar Zamfara da ta tsinci maƙudan kuɗi a kasar Saudiya ta kuma mayar ga hukumomi.
An karrama Auwal yayin gagarumin taron rufe makon tunawa da Sheik Usmanu ‘Danfodi wanda ya samu halartar dubban mutane ciki harda fitaccen malamin addini Musulunci na duniya Sheik Zakir Naik.