Sarkin Gobir ya rasa ransa a hannun ƴanbindiga
Daga Sabiu Abdullahi
Rahotannin da fitowa daga jihar Sokoto na cewa y’an bindigar sun kashe Sarkin Gobir na garin Gatawa, Alhaji Isa Bawa.
Sun kashe shi ne bayan da suka yi garkuwa da shi na tsawon mako 3.
Idan ba manta ba cikin wannan makon ne sarkin ya fito a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya ‘yan bindigar kudin fansa da suka bukata.
A cikin bidiyon, ya ce idan wa’adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.