Sanusi Lamido Sanusi ya sake zama Sarkin Kano karo na 2
Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ba da sanarwar mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano.
Abba Kabir ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan sanya hannu kan dokar da ta yi gyara ga dokar da ta kafa dokar masarautun Kano ta 2019.
Idan ba a manta ba, a yau Alhamis ne Majalisar dokokin ta jihar Kano ta yi wa ƙudurin dokar soke masarautu biyar na Kano, wato Kano, Bichi, Rano, Karaye da Gaya karatu na uku tare da amincewa da ita.
Daga nan ne aka miƙa dokar ga gwamnan wanda ya sanya mata hannu.