January 14, 2025

Sanatocin Kudu Maso Kudu Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Dokokin Gyaran Haraji

0
FB_IMG_1732804020861.jpg

Daga Sabiu Abdullahi
 
Sanatoci daga yankin Kudu maso Kudu sun nuna goyon bayansu ga dokokin gyaran haraji, domin a cewarsu dokokin za su taimaka wajen tabbatar da dorewar tattalin arziki da ci gaba.
 
A wata sanarwa da suka fitar, ‘yan majalisar sun bukaci takwarorinsu daga Arewacin Najeriya da su kauce wa son zuciya tare da nazarin dokokin da aka gabatar.
 
“Mun amince da dokokin gyaran haraji bisa la’akari da mahimmancin gyare-gyare wajen bunkasa kudaden shiga na kasa da kuma tabbatar da dorewar tattalin arziki,” in ji sanarwar.
 
Haka kuma, sanatocin sun jefa kuri’ar yarda ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
 
Sun tabbatar da aniyarsu ta goyon bayansa da kuma marawa jagorancinsa baya.
 
Dokokin gyaran harajin dai sun jawo cece-kuce, yayin da Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa suka nuna adawa da su, suna masu cewa dokokin za su cutar da muradun yankin.
 
Sai dai, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ba za a janye ƙudurorin dokokin daga majalisar ba.
 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *