March 28, 2025

‘Sama da ‘yan Najeriya miliyan 31 na fuskantar matsananciyar yunwa’ 

images (10) (9)

Daga Sabiu Abdullahi   

Wani sabon bincike da gamayyar ƙungiyoyin ci gaban kasa da kasa suka gudanar ya nuna cewa sama da ‘yan Najeriya miliyan 31.8 na fuskantar matsalar karancin abinci, lamarin da ya ta’azzara sakamakon kalubalen tsaro da ake fama da shi da kuma cire tallafin man fetur.   

Ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta tattalin arziki ta bayyana sakamakon binciken, wanda ya nuna tsananin tasirin da ake samu wajen samar da abinci da kuma matsalar rashin abinci mai gina jiki da ke addabar mata da yara.   

Ma’aikatar ta bayyana cewa, “Tashin farashin kayan abinci, sakamakon cire tallafin man fetur da kuma matsalolin tsaro da ake ci gaba da fuskanta, ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.   

Binciken, wanda aka gabatar a taron da aka yi tsakanin abokan huldar ci gaban da kuma gwamnati, ya nuna bukatar gaggawar daukar matakan da suka dace don magance matsalar.   

Sakamakon binciken ya nuna karuwar mutane miliyan 18.6 da Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa za su iya fuskantar matsanancin karancin abinci tsakanin Oktoba da Disamba 2023.   

Matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka na cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023 ya haifar da tsadar sufuri, lamarin da ya haifar da matsalar tsadar rayuwa a Najeriya da ba a taɓa gani ba cikin shekaru da dama.   

Sannan hare-haren ‘yan bindiga da suka hada da maharan da ke dauke da makamai ya tilasta wa manoma da yawa barin gonakinsu, lamarin da ya ta’azzara farashin kayan abinci da hauhawar farashin kayayyaki.   

Sanjo Faniran, babban jami’in kula da tsarin samar da abinci na kasa a Najeriya kuma daraktan ci gaban zamantakewa a ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta tattalin arziki, ya yi nuni da cewa, binciken ya nuna gibin da aka samu, da nasarori, da kalubale, tare da bayar da shawarwarin magance matsalolin. 

3 thoughts on “‘Sama da ‘yan Najeriya miliyan 31 na fuskantar matsananciyar yunwa’ 

  1. Приветствую всех, теперь Casino X есть в Телеграм!
    Свежи новости, ответы на вопросы и эксклюзивные бонусы уже ждут вас.
    Присоединйся сейчас и получите 100% бонус до 2000 долларов!
    Эксклюзивный промокод на фриспины только для наших подписчиков.
    Ищите нас по ID: @casinox_rus
    Или жмите на ссылку: Casino X

  2. Сантехник в Минске — решение любых проблем! Мы предлагаем услуги по ремонту с высоким качеством. Узнайте больше на Сантехник Минск.

Comments are closed.