Sai Tinubu Ya Kammala Shekaru 8 Kafin Mulki Ya Koma Arewa—Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa mulkin ƙasa ba zai koma Arewa ba sai bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adin shekaru takwas a 2031.
Ganduje ya bayyana haka ne a jiya Talata a birnin tarayya Abuja yayin da yake karɓar wata tawaga daga ƙungiyar matasa masu goyon bayan Tinubu daga Arewa.
Wannan na zuwa ne yayin da ake samun rahotannin da ke cewa wasu ‘yan Arewa na shirin haɗa kai don ganin an kawo ƙarshen mulkin Tinubu a 2027.
Da yake yabawa ƙungiyar kan manufofinta da gudunmawar da take bayarwa wajen wayar da kan masu zabe, Ganduje ya tabbatar da cewa APC za ta ba su goyon bayan da suke bukata.
9xfuiu
I like what you guys are up too. Such smart work and reporting! Keep up the excellent works guys I?¦ve incorporated you guys to my blogroll. I think it’ll improve the value of my site 🙂