February 10, 2025

Sabuwar Cutar HMPV Na Cigaba Da Yaɗuwa a China

0
images-82.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

A yanzu haka, Sin tana fama da yaduwar cutar numfashi mai suna Human Metapneumovirus (HMPV), wadda take haifar da alamomi makamantan mura da zazzabin sanyi.

An fara gano cutar a shekarar 2001 a ƙasar Netherlands, kuma a halin yanzu, tana yaduwa a jihohin arewacin Sin yayin wannan lokacin sanyin, lamarin da ya sa hukumomin lafiya daukar matakan gaggawa don dakile ta.

HMPV wata ƙwayar cuta ce mai ɗauke da kwayar halitta ta RNA, wadda ke iya haifar da matsaloli masu tsanani kamar ciwon huhu (pneumonia) musamman ga jarirai, tsofaffi, da kuma masu ƙarancin garkuwar jiki.

Alamomin cutar sun haɗa da tari, zazzabi, toshewar hanci, da gajiya, kuma tana nuna alama tsakanin kwana uku zuwa shida bayan kamuwa.

Cutar na yaduwa ne ta hanyar ɗigon ruwa daga numfashi ko kuma taɓa wuraren da aka gurɓata.

Mao Ning, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, ya bayyana cewa: “Cutar numfashi tana yawaita yayin lokacin sanyi. Amma shekarar nan ta nuna cewa rashin lafiyar ba ta yi tsanani ba kamar bara kuma yaduwar ta ba ta kai yadda ake tsammani ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *