January 15, 2025

‘Saboda Allah na dawo da $10,000 da na tsinta a jirgi,’ cewar ma’aikacin filin jirgi da ya yi tsintuwa a Kano

0
IMG-20240830-WA0007

Daga Sabiu Abdullahi  

Wani ma’aikaci a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano, Auwalu Ahmed Dankade, ya mayar da dala 10,000 da ya samu a lokacin da yake sharar jirgin.  

Adadin kuɗin, wanda ya kai kusan N15m, an gano shi ne a ranar Laraba da rana a cikin wani jirgin kasar Masar.  

A wata hira da jaridar Daily Trust ta Najeriya ta wayar tarho, Dankade ya ce, “An horar da ni cewa kada in dauki abin da ba nawa ba, duk wani abu da ka dauka ba bisa ka’ida ba, za a yi maka hisabi a Lahira.”

Ya danganta abin da ya yi da tarbiyyar da ya samu, inda yake cewa, “Iyayena sun koya mana mu gamsu da duk abin da muke da shi, kuma wannan tarbiyya ta sa na dawo da kuɗin cikin sauki.”  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *