May 16, 2025

Sabbin Dabarun CBN: Rahoton Ayyukan Kuɗi na Shekarar 2024

0
images - 2025-05-04T072659.046

Daga Salmanu Isah Darazo

Bayanan kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) na shekarar da ta gabata, 2024, na cigaba da jan hankalin manazarta tattalin arziki, masana, da kuma gama-garin da ke sha’awar fahimtar alkiblar tattalin arzikin Najeriya.

Waɗannan bayanai na nuni da jajircewa matuƙa wajen samar da daidaiton tattalin arziki, da kuma nasarorin aiwatar da ingantattun manufofi da dabarun sarrafa kuɗi, inganta ajiyar kuɗaɗen ƙasa a waje, ingancin kadarori, rage kashe kuɗi, da kuma uwa uba samun riba mai ƙarfi.

Ɗaya daga cikin manyan alamun yalwatar tattalin arziki shi ne matsayi da kuma bunƙasar asusun ajiyar kuɗaɗen ƙasa a waje. Daga cikin hoɓɓasar da CBN ke yi a wannan fanni ya haifar da sakamako mai ban mamaki, inda zuwa yanzu asusun ajiyar ya ƙaru daga dala biliyan 36.6 a 2023 zuwa dala biliyan 38.8 a 2024. Wannan nasara ba kawai ta tsaya a kan lambobi ba ne; tana nuni da ƙaruwar amincewar cikin gida da kuma ta masu saka jari na ƙasashen waje a tattalin arzikin Najeriya.

Hakan ya samo asali ne daga samun tagomashi a shigowar kuɗaɗe daga masu saka jari da ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje. Haka kuma, samun kuɗaɗen shiga daga gwamnati ya ƙaru sakamakon haɗin gwiwa da Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) da kuma inganta shirin jawo hankalin ’yan Najeriya da ke ƙasashen waje. Wannan nasara a fannin ajiyar na waje tana da matuƙar muhimmanci wajen daidaita darajar Naira da kuma biyan bashin ƙasa na ƙetare, da zama kariya daga girgizar tattalin arziki.

Wannan yunƙuri da jajircewa ta CBN, ta tabbatar da daidaito a fannin tattalin arziki na waje na nuna fahimtarsa game da alaƙar da ke tsakanin tattalin arzikin duniya. Yayin da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen cikin gida daban-daban, samun wannan kariya na ajiyar ƙasa na waje yana ƙara fito daɗorewar tattalin arzikin ƙasa da kuma samar da tushe mai ƙarfi ga ci gaba mai ɗorewa.

Ɗaya daga cikin canje-canje mafi jan hankali a tarihin CBN shi ne yadda babban bankin ya sauya hasara zuwa riba. Bayan fuskantar giɓin kuɗi na Naira tiriliyan 1.3 a 2023, Bankin ya dawo da ƙarfi inda ya samu riba ta Naira biliyan 165 a 2024. Wannan sauyi yana nuna ingancin dabarun gudanar da kuɗi da CBN ke aiwatarwa, ciki har da rage kashe kuɗi da kuma zuba jari cikin basira. Damar Bankin na sarrafa kuɗi cikin hikima ba tare da hana ci gaba ba ya nuna irin kwarewarsa wajen shawo kan matsalolin kuɗi.

Wannan ci gaba na samun riba ya samo asali ne daga matakan da babban ya ɗauka wajen rage kashe kuɗi. CBN ya zaftare kashe kuɗaden da ba dole ba, ya inganta zuba jari da kuma karɓar kuɗi daga harkokin musayar kuɗaɗen waje. Wannan dabara ce da ke ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa, domin tana ƙara ƙarfin CBN wajen tallafawa wasu tsare-tsaren da za su taimaka wajen haɓaka sassa daban-daban na tattalin arziki.

Baya ga nasarar kuɗi, CBN ta mayar da hankali wajen rage bashin da ake bin ta. An rage bashin daga Naira tiriliyan 16.1 zuwa Naira tiriliyan 11.9, wanda ya samo asali daga dawo da bashin da aka bayar a baya da kuma sauya salo daga bayar da rancen tsoma baki. Ta haka ne CBN ke barin kasuwa ta yi rawar gani wajen raba rance, wanda hakan ba ko shakka na inganta tsarin kuɗi gaba ɗaya.

Sauya salon bayar da rance da CBN ya yi zuwa barin kasuwa ta yi tasiri abu ne mai hangen nesa, domin yana taimakawa wajen ƙarfafa gasa tsakanin cibiyoyin kuɗi, wanda hakan na amfanar da masu amfani da su. Wannan ya zo daidai da ƙa’idojin duniya da cibiyoyin kuɗi na ƙasa da ƙasa ke bayarwa, kuma alama ce cewa CBN na da niyyar sabunta hanyoyin aikinsa bisa ƙa’idar zamani.

Rage kashe kuɗi ya kasance babban abin da CBN ta fi mayar da hankali a kai a shekarar 2024, inda aka ga ci gaba sosai. An gudanar da ayyukan cikin tsari domin tabbatar da ingancin amfani da kuɗaɗen Bankin. An rage kashe kuɗi da bai zama dole ba, an kuma ƙarfafa tsarin aiki a rassan CBN daban-daban, wanda hakan ya taimaka wajen inganta sarrafa kuɗi da aiki cikin tsari.

Baya ga haka, aiwatar da tsarin kula da rahotannin kuɗi na cikin gida (ICFR) ya ƙara fito da nagarta da kuma amincin bankin. Wannan ba wai kawai don bin doka ba ne sai dai wani ɓangare ne na haɓaka tsarin shugabanci da kariya daga haɗurran cikin gida.

Ta hanyar daidaita ayyukanta da ka’idojin duniya, CBN ta ƙarfafa amincewa daga jama’a da sauran masu ruwa da tsaki.Yayin da tattalin arzikin Najeriya ke fuskantar ƙalubale da dama – daga sauyin farashin man fetur zuwa rikice-rikicen siyasar duniya, dabarun CBN wajen gudanar da kuɗaɗe sun zama fitilar hure waɗannan ƙalubale. Haɗakar da ingantattun manufofi, basirar sarrafa kuɗi, da gaskiya a aiki na ba da damar fuskantar gaba da kwarin guiwa.

Nasarar da aka samu a shekarar 2024 ba ita ce ƙarshe ba, sai dai matakin farko ne na cigaban da CBN ke shirin aiwatarwa domin tabbatar da daidaiton tattalin arziki. Wannan hangen nesa ya haɗa da sauya Naira, sarrafa ajiyar ƙasa, da kuma samar da yanayin da zai jawo zuba jari, kirkire-kirkire da ci gaba.A taƙaice dai sakamakon kuɗi na CBN na shekarar 2024 wata alama ce mai nuni da daidaiton tattalin arzikin ƙasa.

Mayar da hankali kan aiwatar da ingantattun manufofi, sarrafa kuɗi cikin hikima, da kuma rage kashe kuɗi ya samar da manyan nasarori. Haɓakar ajiyar kuɗi a waje, dawowa daga asara zuwa riba, raguwar bashin da ake bin Bankin, da kuma inganta tsarin kula da kuɗi sun nuna irin kyakkyawan shugabanci da Bankin ke da shi.

Yayin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tattalin arziki, waɗannan cigaban da ake samu na nuni da cewa akwai dabarun magance su. Nasarorin da CBN ta cimma sun kasance abin koyi da kuma alamar mafita mai dorewa. Tare da jagoranci mai ƙarfi da hangen nesa mai zurfi. Najeriya na da damar shawo kan matsalolinta da kuma kafuwar tattalin arziki mai ƙarfi da ɗorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *