January 15, 2025

Rushe masarautun Kano ya haddasa zanga-zanga

0
IMG-20240526-WA0021.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Da safiyar ranar Lahadi ne aka tashi da zanga-zanga a kan titunan masarautar Gaya, ɗaya daga cikin masarautu biyar da majalisar dokokin Jihar Kano ta rushe.

Majalisar dokokin jihar dai ta soke dokar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya yi amfani da ita wajen tsige Muhammadu Sanusi II a shekarar 2020.

Yayin da yake amincewa da dokar a ranar Alhamis, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanar da rushe ƙarin masarautu guda biyar da Ganduje ya ƙirƙiro.


Gwamnan ya kuma umarci dukkanin sarakunan masarautun da suka haɗa da Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, Sarkin Gaya, da su miƙa al’amuran masarautunsu ga mataimakin gwamnan Jihar, Kwamared Abdulsalam Gwarzo, wanda ke kula da ma’aikatar ƙananan hukumomi da al’amuran sarakuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *