February 12, 2025

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta damƙe ‘yan damfara

0
IMG-20240609-WA0031.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

A wata sanarwa da hukumar ‘yansanda ta jihar Kano ta fitar a yau ɗin nan, rundunar ta ce ta sami nasarar damƙe wasu gawurtattun ‘yan damfara waɗanda su ka shahara wajen tura saƙon shigar kuɗi a banki na bogi da sauya ma ‘yan kasuwa POS da katin ATM.

Abubuwan da aka samu a wajen miyagun sun ƙunshi POS 22, ATM 52, jarakunan fetir 8 da wayoyin hannu guda 6.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar Kanon, CP Mohammed Usaini Gumel, ya ja hankalin al’umman jihar musamman ‘yan kasuwa da su sanya idanu sosai saboda irin waɗannan miyagu sannan su gaggauta sanar da hukuma duk lokacin da su ka ga wani abinda ba su gane ba ta hanyar tuntuɓan layukan ko-ta-kwana na rundunar.

Rundunar ta nemi da a gaggauta tuntuɓanta a 08032419754 ko 08123821575 ko kuma 09029292926.

Wannan nasara da aka cimma, inji rundunar ‘yansandan ta samu ne sakamokon “jajircewa irin na dakarun rundunar wajen tabbatar da tsaro a faɗin jihar bayan ƙorafe-ƙorafe da aka kawo ma rundunar daga wajen masu gidajen mai da kuma ‘yan kasuwa kan irin zamba da ɓata-garin ke aikata wajen sayen kaya da biya ta hanyar turo saƙon kuɗi na bogi da kuma sauya ma ‘yan kasuwa na’urar cirar kuɗi ta POS ko katin ATM,” inji sanarwar.

Bayan samu waɗannan ƙorafe-ƙorafe ne rundunar ta samar da zaratan jami’anta waɗanda su ka sanya idanu kuma aka cimma nasaran damƙe mazambatan

Sanarwar ta ambata cewa a ranar 5 ga wannan watan ne rundunar ta sami wani kira daga gidan man Chula Filling Station inda bayan halartan dakarun su ka sami sa’an cafke wani ɗan shekara 38 mazaunin rukunin gidajen Na’ibawa mai suna Abdulkadir Ibrahim da wani mai suna Aliyu Tukur ɗan shekara 27 mazaunin rukunin gidajen Kuntau Kano.

Binciken jami’an tsaro ya tabbatar da cewa ɓata-garin sun sayi mai na ₦300,000 a wannan gidan mai na Chula amma suka biya ta hanyar tura saƙon kuɗin bogi. Waɗanda ake zargin, yayin da suke hannun ‘yansanda sun tona asirin abokan hulɗarsu inda aka wani matashi ɗan shekara 20 mai suna Auwal Ibrahim.

A yayin binciken, kamar yadda rundunar ta tabbatar, “dukkanin waɗanda ake zargin sun tabbatar da cewa sun aikata laifukan da ake zargin su a kai har su ka ƙara da bayyana wasu gidajen man da wuraren kasuwanci mabambanta da su ka sha damfara.

Kwamishinan ya yi godiya ga al’umman na Kano bisa ga goyon baya da haɗinkai da su ke ba jami’ansa, kuma ya tabbatar masu da cewa a yanzu haka ana ci gaba da binciken waɗanda ake zargin, kuma da zarar an kammala za’a gurfanar da su a kotu don fuskantar hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *