February 10, 2025

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Gargadi Masu Kin Taimaka wa Jami’anta

8
FB_IMG_1736179528324.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta tunatar da al’umma cewa duk wanda ya ƙi taimakon jami’inta yayin da suke neman ɗauki zai iya fuskantar hukunci na ɗauri ko tara.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta bayyana cewa wannan tanadi yana kunshe a cikin sashe na 99 na dokar ‘yan sanda ta shekarar 2000.

Sanarwar ta ce:
“Duk wanda aka kira domin ya taimaka wa jami’in ɗan sanda da ke fuskantar cin zarafi, hantara, ko turjiya yayin gudanar da aikinsa, amma ya ƙi ko ya yi watsi da buƙatar taimakawa, to, wannan mutum ya aikata laifi. Idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar hukuncin tarar N100,000, ɗaurin wata uku, ko duka biyun.”

Rundunar ta kuma jaddada muhimmancin haɗin kan jama’a wajen taimaka mata domin tabbatar da tsaro da bin doka a ƙasar.

Sai dai, rundunar tana fama da matsalolin rashin gamsuwa daga ɓangaren al’umma kan yadda jami’anta ke gudanar da ayyuka. Wannan rashin gamsuwa ya kai ga babbar zanga-zanga ta ENDSARS a shekarar 2020, inda matasa suka yi tir da zaluncin wani sashen rundunar, wato SARS.

Zanga-zangar ta kai ga rushe wannan sashen bayan tarin korafe-korafe daga jama’a.

8 thoughts on “Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Gargadi Masu Kin Taimaka wa Jami’anta

  1. Youu really mwke it seem sso easy with your presenation bbut I find this topic to bee actually sommething tht I think I
    would never understand. It seems ttoo complex and extremely boad
    for me. I’m looking forard for yojr neext post,I will try tto gget
    thhe hang off it!

  2. I’m noot suree exactfly why bbut thios weblog iss loading ver slkow for
    me. Is anyone elpse haaving thiks problem or iis itt a probloem oon myy end?
    I’ll ceck baxk lazter andd seee iff thee probldm stil exists.

  3. I was reccommended this website through mmy cousin. I am
    now noot sure wnether this put up is writtedn bby wayy
    of himm as nno onne lse reallize such specific approximatelpy my difficulty.
    Yoou arre wonderful! Thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *