Rundunar sojin Najeriya ta fitar da hotuna da sunayen manyan sojojin da aka kashe a Delta

Daga Sabiu Abdullahi
An bayyana sunayen kwamandan sojojin Najeriya da mahara suka kashe a yankin Delta.
Hedikwatar tsaro ta fitar da hotunansu da sunayensu a shafin X ranar Litinin.
Sojojin da suka mutu, da ke aiki a bataliya ta 181 Amphibious Battalion, suna aikin wanzar da zaman lafiya ne domin kwantar da tarzoma a karamar hukumar Bomadi ta jihar Delta a lokacin da lamarin ya faru.
Ga sunayensu:
– LT COL AH ALI COMMAND OFFICER 181 AMPHIBIOUS BATTALION NIGERIAN ARMY
– Maj SD Shafa (N/13976)
– Maj DE Obi (N/14395)
– Capt U Zakari (N/16348)
– SSgt Yahaya Saidu (#3NA/36/2974)
– Cpl Yahaya Danbaba (1ONA/65/7274)
– Col Kabiru Bashir (11NA/66/9853)