January 24, 2025

Rukunin farko na maniyyatan Najeriya sun tashi zuwa Saudiyya

0
IMG-20240516-WA0007.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar


Rukunin farko na maniyyatan Najeriya su tashi zuwa ƙasar Saudiyya domin fara ibadar aikin Hajjin bana.

Tawagar farkon ta tashi ne daga filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello da ke birnin Kebbi da ke arewacin ƙasar.

Gabanin fara jigilar maniyyatan sai da hukumar ta gudanar da wani ƙwarya-ƙwaryar bikin ƙaddamar da jigilar maniyyatan.

Cikin waɗanda suka halarcin bikin ƙaddamarwar har da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *