June 14, 2025

Rufe Makarantu Saboda Azumin Ramadan Ya Janyo Ce-ce-ku-ce A Najeriya

images-2025-03-03T155350.984.jpeg

Matakin wasu gwamnatocin jihohi a Arewacin Najeriya na rufe makarantu har na tsawon makonni biyar saboda azumin watan Ramadan ya haifar da cece-kuce a tsakanin al’umma.

Idan ba a manta ba, akwai rahotannin da ke cewa jihohin Bauchi, Katsina, Kano da Kebbi sun umarci dukkan makarantun gwamnati da na kudi da su dakatar da karatu domin bai wa dalibai damar gudanar da ibadarsu ba tare da wata matsala ba.

Sai dai wannan mataki ya haddasa rarrabuwar ra’ayi, inda wasu ke ganin hakan na ƙara dagula matsalar yara masu gararamba a Arewacin kasar.

CAN Ta Soki Matakin

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta soki rufe makarantun, tana mai bayyana shi a matsayin matakin da ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

A wata sanarwa, CAN ta ce: “Rufe makarantu na tsawon makonni biyar saboda Ramadan abu ne da zai hana ci gaban ilimi a yankin da ke fama da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.”

Kungiyar ta kuma yi nuni da cewa akwai kasashen musulmi irin su Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da ke ci gaba da gudanar da karatu yayin azumi, sai dai suna rage tsawon lokutan zama a makarantu.

Kungiyar Dalibai Ta Yi Barazanar Zanga-Zanga

Kungiyar Dalibai ta Najeriya (NANS) ta bayyana cewa ba za ta yarda da rufe makarantu har na tsawon makonni biyar ba, tana mai cewa idan ba a janye matakin ba cikin awanni 72, za su gudanar da zanga-zanga.

Shugaban kungiyar na kasa, Usman Barambu, ya ce: “Ba za mu amince a ci gaba da rufe makarantu saboda Ramadan ba. Za mu dauki matakin da ya dace idan gwamnati ba ta janye wannan kuduri ba.”

Ra’ayoyin Jama’a A Kafafen Sada Zumunta

Wannan batu ya haddasa zafafan muhawara a shafukan sada zumunta. Wasu na goyon bayan matakin tare da cewa hakan yana bai wa Musulmai damar gudanar da ibada cikin kwanciyar hankali.

A gefe guda, wasu na ganin matakin na cutar da ɗalibai, musamman ma wadanda ba Musulmi ba.

Wata mai amfani da shafin X ta rubuta: “Idan muka ci gaba da rufe makarantu saboda Ramadan, yaushe dalibanmu za su koyi ilimin da zai fitar da su daga matsin rayuwa?”

Wani kuma ya ce: “Ba matsala a dakatar da karatu a wannan lokaci. Idan har gwamnatocin jihohi sun ga dacewar hakan, dole a mutunta ra’ayinsu.”

Hukuma Ta Yi Shiru

Duk da cewa ana ta sukar matakin, hukumomin da abin ya shafa ba su fito fili sun mayar da martani ba. Ba a samu damar jin ta bakin kwamishinonin ilimi na jihohin da suka rufe makarantu ba, duk da kokarin da aka yi na tuntubarsu.

A halin yanzu, ana ci gaba da muhawara kan wannan mataki, yayin da jama’a ke jiran matakin da gwamnati za ta dauka kan korafe-korafen da ake ta yi.